Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Da Gaske PDP Ta Dakatar Da Kwankwaso Da Magoya Bayansa?


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Ana ce-ce-ku-ce dangane da sanarwar da daya daga cikin rassan jam'iyyar PDP a jihar Kano ya fitar, inda ya ce ya dakatar da tsohon gwamnan jihar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa har tsawon wata uku.

Bangarori biyu ne dai ke takaddamar jan ragamar jam'iyyar ta adawa a jihar ta Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sanarwa ta fito ne daga sakataren jam’iyyar, H. A Tsanyawa wanda ya sanya wa hannu jim kadan bayan zama da masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka yi a ranar Asabar.

Jam’iyyar dai ta bukaci Sanata Kwankwaso ya yi bayanan kare kansa daga zargin aikata manyan laifuka uku da aka shigar akan sa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Laifukan da aka tuhume shi akai sun hada da ta da husuma a taron zaben shugabannin shiyyar arewa maso yamma da aka gudanar a Kaduna ranar 10 ga watan Afrilu.

Sai tuhumar da ake masa kan dirarwa gwamnoni biyu da ke wurin taron da kuma zargin magoya bayan kwankwasiyya da lalata kayayakin da aka tanada don gudanar da wannan zabe a makon jiya a jihar ta Kaduna.

Hakazalika, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa, ta dauki matakin dakatar da sanata Kwankwaso da magoba bayansa ne, biyo bayan korafe-korafen da ta samu inda ta bukaci Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zo ya wanke kansa daga wadannan zarge-zargen da ake masa.

Wani taro da gwamnonin PDP suka yi a Makurdi
Wani taro da gwamnonin PDP suka yi a Makurdi

Jam'iyyar dai ta yi amfani da dokarta ta sashi na 59 sakin sashi na 1, 2, 3, 4 na mulkin PDP wajen daukan wannan mataki.

A yayin hada wannan labari, kokarin ji ta bakin sanata Rabiu Musa Kwankwaso don jin martanin sa kan wannan labari dai ya ci tura.

Babu Wanda Ya Dakatar Da Kwankwaso - in ji daya reshen PDP a Kano

Sai dai jim kadan bayan fitar da wannan matsaya da ake zargin bangaren su Amb. Aminu Wali da fitarwa, kishiyar wannan bangare, ta fito ta yi watsi da sanarwar wacce suka ce ba ta da tushe balle makama.

Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren jam'iyyar ta PDP, reshen jihar Kano Aminu Abubakar Danbatta ta ce, wannan wani yunkuri ne da wasu mutane ke yi na kokarin ganin sun haifar da husuma a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

"Jama'a sun san da cewa, ba su da wani hurumin da doka ta ba su, su tuhumi ko su dakatar da wani mambar jam'iyyar."

"Hedikwatar jam'iyyar ta amince ne da shugabannin PDP, karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi, wanda aka zabe shi bisa doka a bara."

Sanarwar ta yi zargin cewa, rikicin da aka gani a taron shiyya na jam'iyyar a Kaduna, ya faru ne da goyon da bayan bangaren da yake ikirarin ya dakatar da Kwankwaso.

"Saboda haka, dukkan 'ya'yan jam'iyar ta PDP, su yi watsi da wannan labari na bogi, su kuma dauke shi tamkar a matsayin yunkuri na ta da husuma a tsakanin 'ya'yan jam'iyya."

XS
SM
MD
LG