Anyi Girgizar Kasa a Kudancin Mexico

Wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4 ta girgiza Kudancin Mexico ranar Talata 23 ga watan Yuni, inda ta kashe a kalla mutum biyu tare da lalata gine-gine da dama.

Girgizar ta fara ne a kusa da yankin Huatulco da ke gabar tekun Pacific, kuma an ji girgizar a kusan nisan kilomita 700 zuwa cikin babban birnin Mexico City, lamarin da ya haifar da rushewar gine-gine ya kuma sa dubban mutane suka bazama kan tituna.

Hukumomi sun ce, mutum daya ya mutu a lokacin da wani gini a Huatulco ya rushe, na biyu kuma ya mutu bayan da wani gida a kauyen San Juan Ozolotepec ya fadi.

Kamfanin man Pemex na kasar ya ce, girgizar ta haifar da gobara a matatar man kamfanin da ke Salina Cruz amma ba tare da bata lokaci ba aka kashe gobarar.