Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya: Babu Aikin Hajji Ga 'Yan Kasashen Waje


Masallacin Ka'abah da ke Makkah
Masallacin Ka'abah da ke Makkah

Kasar Saudi Arebiya ta bayyana cewa za'a gudanar da aikin Hajjn bana a kasar amma da mutane kalilan kadai, sakamakon yanayin annobar Coronavirus.

Ma'aikatar da ke kula da aikin Hajji ta kasar ce ta bayyana hakan. A cewarta, mutanen da ke zaune a cikin kasar ta Saudiyya ne kawai za su iya gudanar da aikin Hajjin na wannan shekara.

A kowace shekara dai akalla mutum miliyan 2 ne daga duk fadin duniya ke ziyartar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.

Wasu Musulmai kenan a massalacin Ka'abah kafin barkewar Coronavirus
Wasu Musulmai kenan a massalacin Ka'abah kafin barkewar Coronavirus

Za a fara Hajjin na wannan shekara ne a karshen watan Yuli mai zuwa.

To sai dai gwamnatin ta Saudiyya ba ta bayyana adadin wadanda za su iya gudanar da Hajjin ba.

Saudiyyar ta ce ta yanke wannan hukuncin ne saboda kasa samun rigakafi ko maganin cutar Covid-19 ya zuwa yanzu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG