A Japan jami’an kokawar kasar da aka fi sani da “Sumo” sun zoke wasanin na bana saboda abin fallasar tantance wadanda suka sami nasara gabannin ma ayi kokawar,wadda ya tauye martabar gasar mai da’dadden tarihi a kasar.
Kafofin yada labaran Japan sun bada rahotanni jiya Asabar, dake cewa, za’a soke gasar da ake yi a makonni biyu na karshe cikin watan maris.Wan nan ne karona farko da za’a soke gasar, rabonda a yi haka tun 1946,lokacind a aka dakatar da gasar domin a sake gyara dandalin kokawar wadda ya lalace sakamakon yakin Duniya na biyu.
‘Yansandan kasar suna binciken bayanan da suka gano bayan sun kwace woyar celula dake kunshe da sakonni Text da ‘yan kokawar suka aike wa juna.Sakonni sun nuna kamar 'yan kokawa 13 ne suke da hanu a makarkashiyar. 'Yan kokawa biyu,da alkalan wasa sun amince suna da hanu cikin wan nan sililin.
A cikin daya sakonnin,wani dan kokawa ya gayawa abokin karawarsa cewa, "Ya kai duka kamar da gaske,amma daga bisani sai ya mika wuya". Abokin karawarsa ya bada amsar cewa "Na gane",kuma zan nuna 'yar bajinta".
Abin fallasar ya bakantawa 'yan kasar Japan da dama rai wadanda suke sha'awar kallon wasan.Gasar an farota tun shekaru dubu daya da dari biyar da suka wuce,kuma ta samo asali daga addinin gargajiyar Japan da ake kira Shinto.