Dan shekara 33, Di Maria ya bugawa PSG wasa 248 ya kuma zura kwallaye 87, tun bayan da ya koma kungiyar wacce take Faransa daga Manchester United a shekarar 2015.
“Paris Saint-Germain na farin cikin sanar da cewa Angel Di Maria ya rattaba hannu kan tsawaita kwatiraginsa da shekara daya, tare da zabin karin wata shekara.” Wata sanarwa ta PSG ta ce.
A tarihin kungiyar, dan wasa Safet Susic (1982-91) ne kadai ya fi Di Maria yawan taimakawa wajen zura kwallo wanda ya tallafa wajen cin kwallaye 103.
“Ina fatan zan yi fice a tarihin kungiyar.” Shafin PSG na Twitter ya ruwaito Di Maria yana fada.
Shi dai Di Maria ya lashe kofuna 16 da kungiyar ta PSG da suka hada da nasarori a shekarun 2016, 2018, 2019 da kuma 2020.
Ya shiga wasan da suka yi da Barcelona a matsayin dan wasan canji a wasan zakarun nahiyar turai da suka yi a ranar Laraba.
Ita dai kungiyar PSG tana matsayi na biyu a teburin gasar Faransa ta Ligue 1, wato tana bayan Lille da maki biyu kamar yadda shafin wasannin na Sky Sports ya bayyana.