Wannan nasara ta United ta kawo karshen walwalar da City ta yi ta morewa na lashe wasanni 21 a dukkanin gasar da ake bugawa a kasar ta Ingila.
Ita dai United ta je wasan ne a matsayin ‘yar dagaji duba da yadda ta gaza lashe wasanninta uku na baya-bayan nan, amma bugun penarti da ta samu cikin minti dayan farko ya ba ta damar bude ragar City.
Dan wasan City Gabriel Jesus ya doke Anthony Martial na United a kusa da ragar City, abin da ya kai ga ba da bugun daga kai-sai-mai-tsaron-gida wacce Burno Fernandes ya buga.
Sai kuma damar da Luke Shaw ya samu ta karkashin ragar City minti biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda ya zura wata kwallon.
Ita ma dai City ta taka rawar gani musamman yayin da ake shiga tsakiyar zagayen farko, inda har suka mamaye wasan har zuwa kusan karshen lokacin zuwa hutun rabin lokaci.
Wannan nasara ya haura da United saman teburin gasar ta Premier inda ta tsaya a matsayi na biyu a bayan City wacce ta ba ta tazarar maki 11.
City na da maki 65 yayin da United ke da 54.
Madrid Ta Yi Kunnen Doki Da Atletico
A wata karawar cikin gida da aka yi a gasar La Liga ta Spain, an tashi kunnen doki tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid da ci 1-1.
Madrid ta farke kwallon da Atletico ta zura mata gab da ana shirin kammala wasan, lamarin da ya jefa Atleticon cikin hadarin gushewar burinta na lashe kofin gasar.
Louis Suarez ne ya fara zura kwallo a ragar Madrid cikin minti na 15 sai Karim Benzema da ya dawo daga jinya ya farke kwallon cikin minti na 88 a filin wasa na Wanda Metropolitano Stadium. Ita dai Atletico ta mamaye wasan inda ta yi ta zubar da damar da rika samu.
Sakamakon wannan wasa ya sa yanzu Atletico na gaban Madrid da maki biyar yayin da maki uku kacal ke tsakaninsu da Barcelona wacce ke bayan Atletico.
Ita dai Barcelona ta lashe wasanta da Osasuna da ci 2-0 a karawar da suka yi a ranar Asabar.
Yanzu Atletico na da maki 59, Barcelona na biye da ita da maki 56 sai Madrid mai maki 54.