Dukkan kungiyoyin na saman teburin gasar inda yayin da Man City ke jan ragamar teburin da maki 65, Manchester United na biye da ita da maki 51 a gasar.
Idan dai Man City ta lashe wannan wasa, za ta kara fadada tazarar da ke tsakaninta da Manchester United da maki 17, akasin hakan kuma zai ba Manchester United damar rage yawan tazarar da ke tsakaninsu.
City ce dai za ta karbi bakuncin Man United a filin wasa na Etihad, wacce ta lashe wasanninta 20 da suka gabata, tun bayan da ta yi kunnen doki da West Bromwich Albion da ci 1-1 a ranar 15 ga watan Disambar bara.
Ba dai lallai ba ne Paul Pogba ya samu damar buga wannan wasa saboda raunin da ya ji a cinyarsa, amma ana ganin Victor Lindelof zai iya fara buga wasan yayin da kungiyar ke ci gaba da fuskantar matsalar masu tsaron gidanta.
Ita kuwa City a karon farko a wannan kakar wasa, ba ta da wani dan wasa da yake jinya tun bayan dawowar Nathan Ake.
Manchester United, kungiya ce da ta dogara da kwarewar ‘yan wasanta a matsayinsu na gashin kansu, siddabarun da wasu suke ganin bai cika dorewa ba.
Ita kuwa City ta shahara ne wajen kai samame ta kowanne sako idan ta hadu da abokanan hamayyarta.