Zargin tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Shariff da ake na hannu dumu-dumu cikin tallafa ma ‘yan kungiyar Boko Haram, batu ne da zai cigaba da janyo hankalin ‘yan Najeriya duk da cewa shi tsohon gwamnan ya dade yana so ya wanke kansa amma wasu gani suke yi tamkar tatsuniya ce.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Borno Coalition For Good Governance wadda ke da babban Ofishin ta a jihar, ta rarraba wata takarda da ke kiran gwamnatin tarayya da ta gaggauta kama tsohon gwamnan. Wanna takarda dai ta zo daidai ne da lokacin da tsohon gwamnan yayi taron manema labarai yana karyata zargin da dr. Davies ya yi masa na cewa yana da hannu dumu-dumu cikin daukar dawainiyar kungiyar ta Boko Haram. Ya kuma ce sai ya maka Dr. Davies a kotun Australian wato kasar baturen.
Ita dai wannan kungiyar a cikin wasikar da ta rubuta tace, bayan gwamnati ta mika shi ga kotun kasa-da-kasa, ya kamata ta kwace duk kaddarorin da ya mallaka a gida da waje. Ta kara da jan kunnen gwamnatin Najeriya da kada ta bi son rai wajen wanna batun don yin hakan na iya bata mata suna.
Daga karshe kungiyar tace ba tayi mamakin ganin sunan tsohon gwamnan a cikin masu daukar dawainiyar wannan kungiyar ba. Hujjarsu ko itace, duk lokacin da gwamnatin tarayyar ta kafa kwamitin bincike sai an ambachi sunan tsohon gwamnan.
Muryar Amurka ta zanta da Ghali Sule wanda yace in aka yi la’akari za a ga cewa wannan baturen da gwamnati ta gayyato ba ma dan kasar Najeriya bane, kuma zai yi wuya ace duk cikin ‘yan Najeriya babu wanda aka Ambato sunansu daga shi sai tsohon babban hafsan sojan Najeriya. Don haka akwai kashin gaskiya a cikin batun. Ghali Sule ya kara da yin kira ga gwamnati da ta gurfanar da su a gaban kotun duniya.
Tuni dai dama ’yan jam’iyyar APC suka ce a gurfanar da shi tsohon gwamnan gaban kotu, abin da wasu ‘yan Najeriya suka ce adawa ce, saboda da tsohon gwamnan dan a jam’iyyar ne amma ya chanza sheka ya koma PDP.
Your browser doesn’t support HTML5