Ana zargin Kakakin Majalisar Dokokin kasar Indonesiya da kasancewa da hannu a wata tabargazar almundahana ta miliyoyin daloli na shirin katin shaidar zama dan kasa na lataroni.
WASHINGTON D.C —
Shugaban hukumar yaki da almundahana ta kasa, Agus Rahardjo, ya fadi jiya Litini cewa akwai isasshiyar shaidar da ke nuna cewa Kakakin Majalisa Setya Novanto na da hannu a wata almundahana ta sace dala miliyan 170 tsakanin 2011 da 2012, wanda kusan daya bisa ukun dala miliyan 440 da aka ware ma shirin kenan.
A cewar Rahardjo, Novanto, wanda shi ne kuma Ciyaman din jam'iyyar Golkar, ya yi amfani da matsayinsa wajen arzuta kansa da wasu mutane.
Amma a wani taron manema labarai da ya kira yau Talata, Novanto ya karyata zargin.
Akwai wasu jami'an gwamnatin Idonesiya ma da ake zargi da kasancewa da hannu a wannan tabargazar, ciki har da Ministan Shari'a da kuma tsohon Ministan Cikin Gida