Ana Zargin Gwamnatin Syria Da Amfani Bam Mai Guba

Turkish forces and members of the Free Syrian Army are seen on the outskirts of al-Bab, Feb. 4, 2017.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta zargi dakarun gwamnatin Syria da yin amfani da bam mai dauke da sinadarin Chlorine a wasu yankunan fararen hula dake arewacin kasar, akalla sau takwas a karshen shekarar da ta gabata.

A wani rahoto da ta fitar a jiya Litinin, kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce dakarun na Syria sun fara amfani da sinadarin na Chlorine ne tun a ranar 17 ga watan Nuwambar bara, yayin da sojojin kasar dake samun goyon bayan takwarorinsu na Rasha ke kusta kai zuwa yankunan da ‘yan tawaye suka mamaye.

Wani hoton bidiyo da aka hada tare da rahoto, ya nuna yadda wata fashewa ta auku, daga nan kuma sai aka ga wani launi mai ruwan dorawa hade da launin kore ya na bazuwa daga fashewar.

Kungiyar ta Human Righst Watch ta ce akalla mutane 200 ne suka samu raunuka daga wannan fashewa.