Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Koriya Ta Arewa Babbar Matsala Ce - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira Koriya Ta Arewa "babbar matsala" bayan gwajin makami mai linzami da ta yi na baya-bayan nan.

Yayin wata hira da manema labarai a Fadar Shugaban Amurka na White House da Firaministan Canada Justin Trudeau jiya Litini, Trump ya ce gwamnatinsa za ta ladabtar da Koriya Ta Arewa sosai. Amma bai yi cikakken bayani ba.

Trump ya kuma yaba da ganawarsa da Firaministan Japan Shinzo Abe a karshen wannan makon a Florida. Shugabannin biyu na tare ranar Lahadi lokacin da Koriya Ta Arewar ta harba makami mai linzami na baya-bayan nan, wanda manyan jami'an Koriya Ta Kudu su ka ce ya yi tafiyar wajen kilomita 500 kafin ya fada kogin Japan.

Abe ya ya kira matakin na Koriya Ta Arewa "abin da sam ba za a lamunta da shi ba."

Haka zalika, Kwamitin Sulhun MDD ya yi taron gaggawa na sirri don tattaunawa kan harba makami mai lizamin na daren jiya Litini. Kasashen Amurka da Japan da Koriya Ta Kudu ne su ka bukaci a yi wannan taron.

A wata takardar sanarwar bayan taro, Kwamitin yayi tir da kaddamar da makamin da cewa wata sabawa ce ta nauyin da ya rataya a wuyar Koriya Ta Arewa a matakin kasa da kasa a karkashin tanaji na 6 na MDD.

XS
SM
MD
LG