Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NATO Zata Nemi Karin Gudunmawa Daga Mambobinta


A Yau Talata Sakatare Janar na kungiyar Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce zaman tattaunawan da mambobin kungiyar za su yi, zai mai da hankalin ne kan kira ga kowace kasa da ta kara yawan kudaden gudunmuwar da take bayarwa kan harkar tsaro ga kungiyar.

Styoltenberg ya fadawa manema labarai hakan ne a birnin Brussels gabanin taron, inda ya ce kungiyar Tsaron ta NATO ta kara adadin kudin da take kashewa a bara zuwa Dala biliyan Goma, amma kuma kasashe biyar ne kawai daga cikin mambobin kungiyar 28 suka iya ba da gudunmuwar kashi biyu daga cikin kudaden da suke samu a bangaren ababan da suke samarwa a cikin gida.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya sha sukar kungiyar ta NATO a lokacin yakin neman zabe, inda ya yi kukan cewa kadan daga cikin mambobin ne kadai suke iya biyan kudaden.

Akwai lokacin ma da ya taba furta cewa duk kasar da ba ta ba da gudunmuwarta ba, Amurka ba za ta ba ta kariya ba.

Sai dai tun bayan da ya karbi mulki, Trump ya nuna goyon bayansa ga kungiyar ta NATO, a cewar Stoltenberg, inda sau biyu ya jaddada hakan a tattaunawar wayar tarho da suka yi.

A yau Talata, sabon Sakataren Tsaro Jim Mattis zai kama hanya zuwa birnin Brussels domin harlatar taron na NATO.

XS
SM
MD
LG