Ana Zargin Barkewar Cutar Sankarau Ya Hallaka Dalibai 20 A Jihar Yobe 

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

Tashar talabijin ta Channels ta ruwaito cewar, dalibai 20 sun mutu a wasu makarantun sakandaren kwana na ‘yan mata guda 3 da kuma Kwalejojin Gwamnatin Tarayya na ‘yan mata dake kananan hukumomin Potiskum da Fika a jihar Yobe sakamakon barkewar cutar da ake zargin sankarau ce.

Kwamishinan iImin Firamare da Sakandare na jihar Yobe Muhammad Sani-Idris ya shaidawa manema labarai cewar “an tabbatar da rasuwar dalibai 20 a makonnin da suka gabata daga barkewar cutar da ake zargin sankarau ce a makarantun sakandaren kwana dake kananan hukumomin Potiskum da Fika.

Haka kuma an kwantar da dalibai da dama a asibiti amma yanzu an sallame su.”

Har ila yau, Gwamna Mai Mala Buni da ya samu wakilcin Mataimakinsa, Idi Barde-Gubana, ya ziyarci makarantun da al’amarin ya shafa da suka hada da Sakandaren Gwamnati (GSS) dake Fika da Kwalejin Gwamnati ta Koyon Kimiya da Kire-kire da kuma Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Koyon Kire-kire dukkaninsu a Potiskum da kuma Kwalejin Gwamnati ta Koyon Kimiya da Kire-kire dake garin Gadaka a karamar hukumar Fika ta jihar Yobe.

A jawabinsa ga wakilan gwamnatin a asibitin kwararru na garin Potiskum, Babban Sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Isa Bukar ya ce adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai mutum 214 kuma 3 dake bangaren kulawar musamman na asibitin na murmurewa.

Ko a watan Afrilun da ya gabata ma an samu barkewar irin wannan cuta tsakanin al’ummomin garin Degubi na karamar hukumar Fika ta jihar Yobe.