Ana Zaman Zullumi A Yankin Onitsha

Mazauna kudu maso gabashin Najeriya

Rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta lashe takobin tabbatar da tsaron a duk sassan jihar Anambra gabani da baya zaben da za a gudanar a jihar

Hausawa mazaiuna garin Awka, babban birnin jihar Anambra, sun tofa albarkacin bakinsu ga zaben da za a gudanar a jihar gobe asabar idan Allah ya kaimu cike da fatan alheri jama’ar sun bukaci gudanar da zaben cikin kwanciyar hankalin da kuma fatan duk wanda Allah ya baiwa za a taru a rufa masa baya.

Cikin jam’iyyu talatin da biyu (32) da suka shiga yakin neman zaben alamomi na nuna cewa zai fi kasancewa tsakanin jam’iyyun APGA, PDP da APC, a yayinda jam’iyyun PPA da UPP, na ikirarin cewa har yanzu dasu.

Kwamishinan hukumar zabe na kasa mai kula da zaben gobe Mr. Solomon Toyebi, na tabbatarwa al’umar Najeriya, cewa a shirye hukumar take na ganin cewa ta gudanar da zabe na gari.

Ita kuma rundunar ‘yan Sandan ta kasa ta lashe takobin tabbatar da tsaron a duk sassan jihar gabani da baya zaben. Fiye da mutane miliyan biyu ne suka yi rajistan kada kuri’a, a zaben amma yanzu dai ana zaman zullumi a yakin Onitsha, inda ‘yan kungiyar IPOB, dake fafutukar son ballewa daga Najeriya, na cigaba da barazanar hana zaben.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Zaman Zullumi A Yakin Onitsha - 2'36"