Kasancewar munin wannan matsalar ya sa ake cigaba da daukar matakan fadakar da al’ummar Nijar, musamman mazauna karkara akan yadda za a magance wannan matsalar.
Malam Mammane Sani, mazaunin garin Kawara a janhuriyar Nijar, na cikin wadanda suka dukufa wajen wayar da kan mata da mazajesu. Ya ce ya kamata daga wata uku zuwa hudu mace ta fara zuwa awo asibiti.
“Zuwa asibiti na da muhimmanci sosai ga mace mai juna biyu saboda ana kulawa da lafiyar dan dake cikinta har zuwa lokacin da za a haife shi da bayan suna, haka kuma ita ma uwara ana kula da lafiyarta har bayan lokacin da ta haihu”, a cewar malam Salisu Magaji, shugaban asibitin garin Kawara. Ya kuma ce akwai matsaloli dayawa dake tattare da rashin zuwa asibiti ga mai juna biyu.
A wani gefe kuma, kungiyar matasan birnin Konni ta hada jami’an tsaro, da fararen hula, da ‘yan siyasa, da kungiyoyin mata wajen gudanar da ayyukan sa-kai don tsabtace asibitin birnin Konni.
ga karin bayani cikin sauti daga Haruna Mamman Bako.
Facebook Forum