Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mugabe Ya Ki Amincewa Da Matakin Sojan Kasarsa


Al’ummar kasar Zimbabwe sun shiga kwana na biyu a yanayin rashin tabbas game da harkokin siyasar kasar, yayinda ake rade radi kan lokaci da kuma yadda shugaba Robert Mugabe zai mika mulki, a bayan da ya shafe kusan shekaru arba’in yana shugabanci.

Jami’an sojin kasar Zimbabwe sun yiwa shugaba Mugabe daurin talala jiya, suka kuma kwace ikon kasar dake kudancin Afrika a wani juyin mulkin da ba a zubda jini ba.

Wadansu sun yi na’am da kawo karshen mulkin Mugabe.

Majiyoyi na nuni da cewa, Mugabe, wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya da shekaru casa’in da uku, yaki mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya. Rahotanni da dama sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa Emmerson Mnangagwa, da shugaban hamayya Morgan Tsvangirai dukansu sun koma gida daga gudun hijira na radin kansu da suka tafi, da nufin taka rawa a sabuwar gwamnatin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa, ana tsare da Mugabe da matarsa Grace a fadar shugaban kasa dake Harare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG