‘Yan kasar Zimbabwe na fatan ganin an sasanta rikicin siyasar kasar cikin gaggawa ba tare da wata tangarda ba, yayin da bangaren ‘yan adawa, da kungiyoyin fararen hula da na addinai suka yi kira ga dadadden shugabansu Robert Mugabe ya yi murabus bayan da sojoji suka karbe ikon mulkin kasar.
Sai dai rahotanni a jiya Alhamis sun ce, Mugabe na nuna turjiya, yayin da shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya kore duk wani burin ganin an dauki wani matakin karshe, yana mai fadawa majalisar dokokin kasarsa cewa, “ya yi wuri a dauki wata kwakkwarar matsaya a yanzu.”
Shugaba Mugabe bai fito baina jama’a ba, tun bayan da sojoji suka yi mai daurin talala a Harare a daren Talata.
Masu shiga tsakanin da Afirka ta Kudu ta tura, sun je gidan Mugabe da kuma Fadar shugaban kasar a jiya Alhamis.
Su dai sojojin kasar ta Zimbabwe, sun jajirce cewa, ba juyin mulki suka yi ba, lamarin da kungiyar tsoffin wadanda suka yi wa kasar fafutukar suka kwatanta a matsayin “yin gyara ba tare da an zub da jinni ba.”
Facebook Forum