Ana Tarwatsa Sansanonin Mayakan Boko Haram Dake Sambisa

Hedikwatar tsaron Najeriya,tace ana samun nasara wajen tarwatsa sansanonin mayakan Boko Haram dake dajin Sambisa, wannan ya biyo bayan hadin kwiwar dake tsakanin Jami’an tsaron Najeriya, da kasashe makwabta inda aka tura jami’an tsaro zuwa wasu yankunan da aka kwato daga mayakan na Boko Haram.

Mukaddashin daraktan dake hulda da jama’a, na hedkwatar tsaron Najeriya, Kanar Sani Usman Kuka sheka, ya shedawa Wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul’Aziz, cewa rundunar sojojin Najeriya suna ci gaba da watsa sansanonin mayakan Boko Haram dake dajin Sambisa,a wani sabon yunkuri na kawo karshen matsalar Boko Haram.

Hedkwatar tsaron ta gargadi jama’a, ta bakin Kanar Sani Usman, da ake sa ido domin magance matsalar tashin boma-bomai wanda ake samu a jihohin Borno Yobe da jihar Adamawa, yana mai cewa ”tunda an tarwatsa sansanoninsu yanzu su kan so su gudu su saje da jama’a, saboda haka mutane dole ne su kula da tsaro, domin harkar tsaro bawai akan jami’an tsaro kawai ya ta’allaka ba kowa nada gudunmawa da kuma hakki akai.”