Ana ci gaba da juyayin rasuwar Dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule wanda ya riga mu gidan gaskiya a jiya Litinin.
A kuma yau Talata ake sa ran za a yi jana'izarsa bayan an dawo da gawarsa daga kasar Masar inda ya kwanta wata 'yar gajeruwar jinya.
Bayanai daga iyalansa da kuma majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa ya rasu ne dalilin matsalar bugun zuciya.
Dan Masanin Kano mutum ne da aka san shi barkwanci da sanin darajar mutane kamar yadda wasu aminansa kamar su Dr Junaidu Muhammad da Farfesa Dan Datta Abdulkadir suka fadawa wakilin sashen Hausa a Kano, Mahmud Ibrahin Kwari.
Su ma 'ya'yan marigayin sun yi kyakkyawar shaida ga mahaifinsu bisa ga irin tarbiya da ya basu na su tashi su nemi abin kansu.
Alhaji Muntari Maitama Sule na cikin manyan 'ya'yan marigayin, ya kuma ce mahaifinsa bai taba nemarwa 'ya'yansa wata alfarma daga kowa ba, sai dai ya basu kwarin gwuiwa su zage dantse su nema na kansu.
Abokin aikinmu Aliyu Mustapha Sokoto ya tuntubi wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, kan halin da ake ciki dangane da jana'izar, ga kuma yadda tattaunawarsu ta kaya:
Your browser doesn’t support HTML5