An dai shafe kwanaki 2 ana gudanar da wannan taro da kuma bita akan yadda za a inganta aikin Hajji wanda ako wane shekara ake kokarin bunkasa shi.
Uba Mana shine babban jamiin watsa labarai na hukumar Alhazan.
Yace, ‘’Yau mun kai shekaru 10 gaskiya abin yabo ne domin munyi abubuwa da dama alal misali a yau ba zaka ji ance Alhaji Najeriyan an bar shi a tashar jirgi ba, ba zaka ji cewa Alhaji ba a kaishi akan lokaci ba , ba zaka ji gwamnatin tarayyar Najeriya na rokon Gwamnatin kasar Saudiya ta bamu lokaci ko mu dauki Alhazan mu zuwa gida Najeriya ko kuwa mu kaisu Saudiyya ba A yau ba zaka ji ana kukan cewa ana kukan jirgi kaza ya bar mutane kaza ba, ba zaka ji jiragen kanfanonin yawo sun cuci wani ba tare da hukumar Alhazai ta shigo ta mangance wannan abu ba, abubuwa da dama gaskiya sai hamdala’’
Jawabin bayan taro ya nuna cewa korafe-korafen rage kudin Hajjin bai samu karbuwa ba saboda hauhawar musayar kudi ta Naira da kuma Dala da ake anfani dasu.
Sakataren hukumar Bello Tambuwa yace tashin farashin Dala data ci karfin Naira ya sanya dole ayi hankuri da wannan farashi na kudaden kujeri manya da kuma kanana na Mahajitta
Ga Madina Dauda da Karin bayani 3’59
Facebook Forum