Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da An Dauki Akidar Sardauna Da An Samu Amsar Rikicin Najeriya Inji Maitama Sule


Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule
Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule

A wata tattaunawar da yayi da Muryar Amurka Marigayi ya ce in da an bi akidar Sardauna da an samu masalaha daga duk rikicin da Najeriya ke fuskanta

Yana mai cewa rikicin addini da na siyasa da na kabilanci duk da an samu masalaha daga garesu idan da an bi irin akidar Sardauna Sir Ahmadu Bello firimiyan farko na arewacin Najeriya.

Yace kungiyar da suka fara yi a arewa a watan Yuni na shekarar 1949 kafin ta zama ta siyasa ita ce NPC kuma shugabanta shi ne Dr. R.B Dikko kuma Kirista ne.

Yayinda kungiyar ta zama ta siyasa Sardauna, Sir Ahmadu Bello, ya kama shugabanci amma kuma likitansa mai duba shi Dr. Ishaya Aude ne wanda Kirista ne. Mai kula da sha'anin tsaro a ofishinsa shi ne Dr Sunday Awoniyi wanda shi ma Kirista ne Bayerabe daga yankin Kaba.Makwafcin Sardauna kuma na hannun damansa wanda ya kasance wazirinsa Michael Audu Buba, shi ma Kirista ne mutumin Shendam daga Filato. Cikin sarakuna babban amininsa shi ne sarkin Kagoro Gwamna Awan, shi ma Kirista ne daga kudancin Kaduna.

Ya cigaba da cewa Kiristocin da ya lissafa su ne suke tare da Sardauna kuma bai tsangwamesu ba bai kuma nuna masu kyama ba. Yace a tuna Sardauna daga zuri'zr Shehu Usman Dan Fidio ya fito kana a lokacin shi ne kuma mataimakin shugaban kungiyar musulman duniya gaba daya yayinda sarkin Saudiya ke shugabancin kungiyar.

Sardauna, a sha'anin addini ya kawo amsa. Shi ya tsaya ma aka kafa kungiyar Kiristocin arewa wadda ta rikide ta zama ta kasa gaba daya. Sardauna ya zauna da kowa kuma ya ba kowa hakkinsa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG