Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Akan Shugaba Buhari Aka Fara Ba


Duk wanda ya kaga batun cewa ana kashe fam dubu hudu akan jirgin shugaban kasa bai san yadda shugabanin duniya ke tafiyar da harkokinsu ba.

Fadar shugaban Najeriya Aso Rock, ta musanta rade raden cewa jirgin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake London na lashe fam dubu hudu duk rana kamar yadda wasu ke yayatawa.

Kakakin shugaban Garba Shehu, yace duk wanda yasan lamarin zirga zirgar shugabani a duniya ba zai kaga wannan labari ba.

Jirgin shugaban da ake Magana aka NAF 001, shi ya kai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari London a watan mayu indai yake zaune har lokajin da jikinshugaban ya warware domin dawowa bakin aiki.

Malam Garba Shehu, yace dayawa jiragen shugabanin ana tsamesu daga biyan haraji wurin tsayawar jirgin su kuma kasashen da ke karba basu wuce amsan fam dubu daya wato ya kasance daya bias hudu na kudin da ake Magana.

Haka kakakin yace ba a kan shugaba Buhari aka fara samun jirgi yana jiran shugaba ba kuma ba a kansa za a den aba ya ganin cewa salon gyara na shugaba Buhari ne wasu ke hamayya da ita.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG