Ana Shirin Kwaso Rukunin 'Yan Najeriya Na Biyu Daga Sudan

Wasu 'yan Zimbabwe da aka kwaso daga Sudan

Sai dai rahotanni na cewa, rukunin farko da aka kwaso ya makale a kan iyakar Masar, bayan da hukumomin kasar suka hana shi shiga kasar ba tare da takardun biza ba.

Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM, ta ce a ranar Asabar za ta kwaso rukuni na biyu na ‘yan Najeriya da yakin Sudan ya rutsa da su.

Mafi aksarin ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan dalibai ne.

“Ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan na mai sanar da dukkan ‘yan Najeriya da ke bukatar a kwashe su cewa a ranar 29 (Asabar) ga watan Afirlun 2023, ofishin jakadancin zai fara kwasar jama’a a karo na biyu zuwa Masar, inda daga can za a dauke su a jirgin sama zuwa Najeriya.

“Duk wanda yake da bukatar tafiya, ya zo Jami’ar Al Razi (Al Azhari) da ke titin Madani da safe. Ba a so mutum ya ruko sama da jaka daya.” In ji wata sanarwa da NIDCOM ta fitar dauke da sa hannun jakadan Najeriya a Sudan, H.Y. Garko a shafin Twitter a ranar Juma’a.

A farkon makon nan Najeriya ta kwaso rukunin farko inda aka nufi kasar Masar da su.

Sai dai rahotanni na cewa, rukunin farko da aka kwaso ya makale a kan iyakar Masar, bayan da hukumomin kasar suka hana shi shiga kasar ba tare da takardun biza ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, akwai akalla mutum 7,000 daga kasashe daban-daban cikinsu har da ‘yan Najeriya, da suka makale akan iyakar suna neman a bar su su shiga Masar.

Hukumar ta NIDCOM ta yi kira ga hukumomin Masar da su bude iyakarsu bisa la’akkari da taimako na jin-kai don jama’a su samu shiga kasar.