A wani al'amari mai kama da shirin shugabanci na mutu-ka-raba, jam'iyyar kwamines mai mulkin kasar na shirin cire wa'adi a kundin tsarin mulkin kasar.
WASHINGTON D.C. —
Babban Kwamitin Jam’iyyar Kwaminist ta China, ya gabatar da shawarar cire wa’adi ga Shugaban kasa da Mataimakinsa daga kundin tsarin mulkin kasar, a cewar kafar labaran gwamnati ta Xinhua.
A yanzu abin da kudin tsarin mulkin kasar y ace shi ne Shugaban Kasa da Mataimakinsa za su yi muki ne da ba zai wuce “wa’adoji biyu a jere ba” na tsawon shekaru biyar-biyar.
Wannan canjin zai bai wa Shugaban China Xi Jinping damar cigaba da zama bisa gadon mulkin har bayan 2023. Tun daga 2013 ya ke Shugabanci.