Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Amnesty Ta Soki Trump a Rahotonta Na 2017


Tambarin kungiyar Amnesty international mai kare hakkin bil adama
Tambarin kungiyar Amnesty international mai kare hakkin bil adama

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta fitar da rahotonta na shekara-shekara, kan yadda ake taka hakkin bil adama a kusan kasashen 160, tana mai ikrarin cewa shekarar 2017, ita ce shekarar da aka fi ganin nuna kiyayya irin ta siyasa, da kuma yadda wasu shugabannin duniya suka jefa fargaba a zukatan mutane.

A wannan sabon rahoto da ta fitar, kungiyar ta Amnesty ta ce, wasu matakai da shugabannin suka dauka a kasashen Masar da Philippines da Venezuela da China da Rasha da kuma Amurka, sun take hakkokin bil adaman miliyoyin jama’a.

Rahoton ya ce, dangane da kasar Philippines, shugaban kasar Rodrigo Deterte, ya fito karara ya yi kira ga mutane da su kashe wadanda ake zargin suna dillancin muggan kwayoyi.

Rahoton kuma ya caccaki shugaban Amurka, Donald Trump, kan matakan da yake dauka na shige da fice a kasar, da tauye walwalar ‘yan jarida da kuma irin tarihin da ya kafawa kansa, dangane da hakkokin mata.

Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin Fadar shugaban kasa ta White House, kan wannan rahoto na kungiyar ta Amnesty, amma haka ba ta cimma ruwa ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG