Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tace Bata Goyon Bayan Amurka a Kan Batun Makaman Nukiliyan Iran


A jiya Litinin ministan harkokin kasashen wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce Rasha bata goyon bayan shugaban Amurka Donald Trump, kan kiran a sake shata fasalin yarjejeniyar kasa da kasa da ta takaita shirin Nukilyar kasar Iran.

Ranar Juma’a ne Trump ya ce wannan shine karo na karshe da zai janye daga sakawa Iran takunkumin da Amurka ta amince ‘dagewa karkashin yarjejeniyar shekarar 2015, domin baiwa ‘yan Majalisa da kasashen Turai kwanki 120 su samu hanyar gyara abin da ya kira “ábubuwan da suka lalace” a cikin yarjejeniyar.

Lavrov ya fadi jiya Litinin cewa idan har Trump ya ci gaba da aiwatarda abubuwan da yake barazanar yayi na ficewa daga yarjejeniyar, akwai mummunan sakamako da ka iya biyo baya, tunda ba shakka Iran zata daina aiki da ka’idojin yarjejeniyar.

Amurka da Rasha da Birtaniya da China da Faransa da kuma Jamus sune suka hada kai suka samar da yarjejeniyar domin tabbatar da ganin cewa Iran bata ci gaba da shirin Nukiyarta ba wajen yin makamai. Iran dai ta nace cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG