Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Indiya Zai Iya Zamowa Mafi Saurin Bunkasa A Duniya


India
India

Kasar Indiya ta yi hasashen cewa tattalin arzikinta zai karu da maki 7.5 a wannan shekara, wanda hakan zai ba ta damar komawa kan matsayinta na kasa mai tattalin arzikin da ya fi bunkasa cikin gaggwa a Duniya.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Indiya ta ke kokarin kakkabe tasirin da soke kudaden takardu da ta yi da kuma wasu sauye-sauye da ta samar a fannin karban kudaden haraji.

Wannan hasashe da Indiya ta yi, wacce ita ce kasa ta uku mafi girman tattalin arzikin a yankin Asiya, ya yi daidai da hasashen da Babban Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na Duniya, wato IMF, suka yi a kwanan nan.

Wannan kuma labari ne mai dadi ga kasar ta Indiya, lura da cewa bunkasar tattalin arzikin kasar ya yi kasa cikin shekaru uku a jere, lamarin da ya sa ya zama koma baya idan aka kwatanta shi da na China, kasar da Indiyan ta bugi kirjin cewa za ta wuce ta a fannin bunkasar tattalin arziki a shekarar 2015.

Jinkirin da bunkasar tattalin arzikin na Indiya ya fuskanta a baya-bayan nan, ya yi hannun babbar riga da yadda tattalin arzikin wasu kasashe ke ganin ci gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG