Ana Samun Sabani Ra'ayi Akan Bude Iyakoki Domin Abinci Ya Wadata

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari wanda gwamnatinsa ta ayyana dokar rufe iyakokin kasar domin hana shinkafa shigowa tare da wasu kayan

Biyo bayan tsadar abinci tun lokacin da gwamnatin Buhari ta hana shigo da shinkafa kasar ta kan iyakokin Najeriya shugabannin jama'a da sarakuna da na addinai suke kiran shugaba Buhari da ya sake tunane akan dokar.

Muryar Amurka ta saurari ra'ayoyinsu mutane dangane da wannan doka da ta haddasa tsadar abinci inda farashin buhun shinkafa ya tashi daga nera dubu takwas zuwa nera dubu goma sha takwas ko ma fiye da hakan.

Wani Haruna Useni da yake sana'ar canji da yanzu jarinsa ya karye yace a karamar hukumarsa wani sau daya zai ci wani ganye da ake kira yadiya kuma ba zai sake cin abinci ba sai dare, kuma da daddaren bai san abun da zai ci ba.

Kiraye kirayen da shugabannin addini da sarakuna da al'umma ke yi na cewa a bude iyakokin kasar domin a samu shinkafa ta shigo, yana cin karo da sabanin 'ra'ayoyi.

Wasu na cewa bude iyakoki domin abinci ya wadata shi ne mafi a'ala yayinda wasu kuma na ganin cigaba da rufe iyakokin shi ne zai sa manoman kasar su tashi su wadatar da kasar da shinkafa da sauran cimaka.

Tanko Iya tsohon ma'aikacin gwamnati yace lalaci da shagwaba sun bata mutane kasar yanzu kuma suna son su yi watsi da baiwar da Allah ya yiwa kasar ta hanyar hana abinci shigowa daga kasashen waje. Dokar da shugaban kasa ya kafa ita ce zata kai kasar ga matakin habaka ta fannin noma. Yace a cigaba da sayen shinkafa da tsada har lokacin da za'a yi tunanen yadda za'a inganta ta gida ta zama kamar ta kasashen waje.\

Shi ma Manjo Janar Patrick Adamu Aspa na goyon bayan cigaba da rufe iyakokin don ra'ayin bayan tsanani akwai sauki. Yace tsadar kayan abinci na sanya manoma su koma gona domin rage dogaro ga man fetur abun da zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Amma limamin wani masallaci a Abuja yace shi ba haka yake ganin lamarin ba. Ya bada misali da lokacin Annabi Muhammad (SAW) yadda ake zuwa kasashen waje a shigo da abinci a duk lokacin da aka samu karanci. Yace ya kamata gwamnatin Buhari ta yi koyi da wannan. A bude iyakoki a shigo da abinci amma kuma a dinga raya shinkafar cikin gida har ta wadatu kafin a dakatar da ta waje. Kafin kasar ta wadatu da abinci kada gwamnati ta bari wasu su mutu da yunwa ko su koma barayi saboda yunwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Samun Sabani Ra'ayi Akan Bude Iyakoki Domin Abinci Ya Wadata - 2' 57"