Ana Sa Ran Trump Ya Tsaurara Dokar Shige Da Fice A Ranarsa Ta Farko Kan Karagar Mulki

Katangar Trump

Ana sa ran zabebban shugaban Amurka Donald Trump ya dauki dimbin matakan zartarwa a ranarsa ta farko a fadar white house domin tsaurara dokokin shige da fice tare da rushe babban shirin Joe Biden na shiga kasar ta hanyar doka, kamar yadda wasu majiyoyi 3 da suka fahimci batun suka shaidawa Reuters

Matakan zartarwar zasu kara baiwa jami’an shige da fice na tarayya karin damar kama mutanen da basu da tarihin aikata laifi, tare da kara yawan dakaru a kan iyakar Amurka da kasar Mexico da kuma ci gaba da ginin katangar dake kan iyakar, a cewar majiyoyi.

Ana sa ran Trump ya kawo karshen shirye-shiryen Biden na bada agaji da suka baiwa dubun dubatan bakin haure damar shiga Amurka a bisa doka a shekarun baya-bayan nan tare da karfafawa wadanda takardunsu suka daina aiki damar barin kasar a bisa radin kansu, a cewar majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu.

Matakan zartarwar Trump na fari zasu zaburar da manufarsa akan shige da fice, wacce ta kunshi alkawarin tasa keyar dimbin bakin haure da shiga Amurka ba bisa ka’ida ba zuwa kasashensu.

Oyalar US-Mexico

A cewar ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka akwai kimanin bakin haure miliyan 11 dake rayuwa a Amurka ba bisa ka’ida tun 2022, adadin daka iya karuwa.

Wasu biranen dake karbar bakuncin bakin hauren ciki harda New York da Chicago da Denver na fama wajen sama musu matsugunai da basu tallafi.

-Reuters