Wani babban jami’in Isra’ila da ministan wajen Lebanon sun bayyana fatan cewar za’a iya cimma yarjejeniya, domin sassauta al’amura a fagen daga na 2 da rundunar sojan Isra’ila ke fafatawa a daidai lokacin da take yakar kungiyar Hamas a gaza.
Ana sa ran majalisar yakin Isra’ila wacce zata zauna da yammacin yau Talata ta amince da wata matsaya a ganawar da Firai Minista Benjamin Netanyahu zai jagoranta, a cewar wani babban jami’in Isra’ila.
Hakan zai share fagen ayyana tsagaita wuta daga Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, kamar yadda wasu manyan majiyoyin Lebanon suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters a jiya Litinin.
A yayin wani taro a birnin Rome, ministan harkokin wajen Lebanon Abdallah Bou Habib ya bayyana fatan za’a kulla yarjejeniyar kawo karshen mummunan yakin Gaza da yayi naso a daren yau Talata.
-Reuters