Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra’ila Ta Kai Mummunan Hari A Tsakiyar Birnin Beirut Na Lebanon


Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu

Wasu hare hare ta sama da Isra’ila ta kai tsakiyar Beirut a ranar Asabar  ya kashe akallah mutane 15 cewar jami’ai, a daidai lokacin da ake cigaba da ganin wasu hare haren a cibiyar babban birnin Lebanon.

Wasu hare hare ta sama da Isra’ila ta kai tsakiyar Beirut a ranar Asabar ya kashe akallah mutane 15 cewar jami’ai, a daidai lokacin da ake cigaba da ganin wasu hare haren a cibiyar babban birnin Lebanon da a baya ba’a saba gani ba a kai a kai, ba tare da wani gargadi da ga Isra’ilan ba, yayin da bangaren diplomasiyya ke fadi tashin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon tace, mutane 63 suka jikkata sakamakon harin, wanda shine hari na 4 a tsakiyar Beirut a kasa da mako guda.

Rincabewar rikicin yazo ne, bayan da wakilin Amurka Amos Hochstein ya ziyarci yankin domin neman cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da zai kai ga karshen watannin da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin Isra’ila da Hezbollah da ya rikide ya zama gagarumin yaki.

Ruwan bamabaman da Isra’ila ta keyi, ya halaka mutane sama da 3,500 a Lebanon, cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon. Hakazalika fadan ya dai dai ta kimanin mutane milyan 1 da dubu 200, ko kwatan mutanen Lebanon baki daya. A bangaren Isra’ila kuwa, kimanin sojoji 90 da kusan farar hula 50 ne suka mutu har lahira, sakamakon Ruwan bamabamai a Arewacin Israila.

Harin na baya bayan nan da aka kai da misalign karfe 4 na asuba, yayi fatafata da wani ginin bene mai hawa 8 a tsakiyar Beirut. Wani jami’in Hezbollah Amin Shiri yace, babu wani jami’in Hezbollah dake cikin ginin. Harin ya taba wasu gine gine dake kusa, inda mutane suka rika Kallon abinda ke faruwa cikin motocin da aka yagalgala a wurin.

Wani jami’in hukumar tsaron farin kaya ta Lebanon Walid Al-Hashash yace, yankin wuri ne dake makare da gidajen zaman jama’a, da matsatstsun hanyoyi da yasa lamarin ya kasance mai cike da kalubalen gaske.

Sojin Isra’ila basu ce uffan ba game da wadanda harin ya rutsa da su.

Hakazalika a ranar Asabar kafar yada labarun kasar tace, wani harin jirgi mara matuki ya kashe mutane biyu da jikkata wasu uku a birnin Tyren na kusa da ruwa dake yankin kudanci.

Mai magana da yawun bangaren Fatah Palasdinu a yankin Tyre, Mohammed Bikai yace, wadanda aka kashe din Palasdinawa ne yan gudun hijira dake sansanin yan gudun hijira na Rashidieh dake kusa, wadanda suka fita kamun kifi.

Bikai yace, duk da dai sojojin Isra’ila sun fitar da gargadi a karshen watan jiya cewa, a kiyayi zuwa yankin gabar Ruwan Lebanon, to amma ba yadda za ayi a gaya ma mai bukatar cin abinci cewa, kar ya fita kamun kifi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG