Ana Kokarin Rage Tsadar Maganin Sankaran Mara

Wasu 'yan mata

Yana yiwuwa ‘yan mata da yawa a kasashe masu tasowa zasu iya samun rigakafin sankaran mara mai arha ta dalilin wani kokari da ake yin a rage tsadar maganin.
Yana yiwuwa ‘yan mata da yawa a kasashe masu tasowa zasu iya samun rigakafin sankaran mara mai arha ta dalilin wani kokari da ake yin a rage tsadar maganin.
Kimanin mata dubu dari biyu da saba’in ne suke mutuwa kowacce shekara ta dalilin cutar sankaran mara, da yawa daga cikinsu a kasashe masu tasowa. Ana daukar irin wannan cutar ne ta hanyar jima’i kuma kwayar cutar tana dadewa a jikin mutum kafin ta zama kansa.

Kasashen da suka ci gaba suna iya amfani da na’urori na zamani su gano cutar da sauri kafin ta yi yawa a jiki yadda za a iya cire ta ba tare da ta zama da illa ga mata ba.

Kwararru sun ce idan aka dauki matakin shawo kan cutar, zai taimaka wajen rage matuwar mata ta dalilin kamuwa da cutar. Kwararru sun ce ‘yan mata miliyan talatin zasu iya samun maganin a shekara ta dubu biyu da ashirin.

Bisa ga shirin da ake yi tare da hain kamfanonin sarrafa magunguna na Merck da GSK, za a iya samar da rigakafin cutar a kan kasa da dala biyar a maimakon sama da dala dari da ake sayarwa a halin yanzu.