Cibiyar yaki da ciwon shan inna tace.wannan ne tsari na farko da aka kaddamar da nufin yaki da kowanne irin nau’in kwayar cutar shan inna. Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa wadansu lokuta kwayar cutar da rigakafin da ake digawa a baki yake kwantarwa tana kin jin magani ta sa kananan yara su kamu da cutar shan inna daga baya, dalili ke nan da yasa aka gabatar da wannan sabon tsarin.
Idan aka sami kudin da ake bukata na aiwatar da wannan sabon shirin,, za a yiwa kimanin sama da kananan yara miliyan dubu dari rigakafi, wanda kuma bisa ga cewarsu zai zama matakin farko na shawo kan cutar. Kwararru suna kyautata zaton cimma nasara wajen kawar da cutar baki daya.
A halin yanzu dai kananan yara goma sha tara ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar shan inna a duniya, adadin mafi kankanta da aka taba samu a tarihi.