Haka kuma a cikin rahoton kungiyar ta Save the Children ta jera kasashe bi da bi daga ta daya zuwa ta karshe game da jin dadin rayuwar uwa da dan ta.
Kasar Finland ce ta daya a jerin kasashen duniya mafiya dadin rayuwa ga uwa da dan ta.
Kasar jamahuriyar Demokradiyar Congo kuwa ita ce mafi rashin jin dadin rayuwa ga uwa da dan ta.
Amurka ce ta talatin a duniya ta na biye da duka kasashen yammacin turai, da Australia da Slovenia da Singapore da New Zealnad da Estonia da Canada da Jamahuriyar Czech da Israila da Belarus da Lithuania da kuma Poland, dukan su sun tsere Amurka a jin dadin rayuwar uwa da dan ta.