An yi kiyasin cewa kusan mutane miliyan uku da dubu dari tara ne suke dauke da kwayar cutar a Najeriya wanda yake isalin kashi hudu bisa dari na yawan wadanda suke dauke da cutar a duniya.
Daga cikin wadanda suke kamuwa da cutar a lokutan baya kuma, kashi goma bisa dari jarirai ne da suke daukar cutar daga iyayensu ko dai lokacin haihuwa ko kuma shayarwa. Sai dai matakan da aka dauka na jinya da tallafawa mata masu ciki ya taimaka wajen rage yawan jariran da suke kamuwa da cutar zuwa kashi biyu zuwa dari.
Kwararru sun bayyana cewa gwaji domin sanin ko mutum yana dauke da kwayar cutar ko babu, da kuma shan magani da zarar ya gane yana dauke da cutar yana taimakawa wajen ceton rayuka da kuma rage yada cutar.