Mafi akasarin jihohin kasar Amurka sun dauki sabon salon kare kuri’oin ‘yan kasar, tsarin dai zai ba gwamnatin tarayya damar lura da yadda zabe ke gudana a jihohin, don magance matsalar satar kuri’a. Kimanin shekaru biyu kenan da kasar Rasha ta taimaka wajen satar kuri’un ‘yan kasar a jihohin Illinois da Arizona.
Gwamnatin kasar ta samar da wani sabon tsari da zai rika lura da yadda mutane ke kada kuri’un su, wanda za’a rika tantance masu jefa kuri’un a lokacin zabe, musamman zaben da za’a gudanar a cikin shekara mai zuwa.
Sabuwar manhajar da gwamnatin kasar ta saya mai suna ‘Albert Sensors’ wanda cibiyar binciken ayyukan yanar gizo ke lura da aikin ta akan kudi dallar Amurka $5,000 kowace guda daya.
Kamfanin mai zaman kansa zai taimaka wajen ganin an magance matsalar satar kuri’a, kamfanin na da kwarewa ta musamman wanda yake aiki da kamfanoni wajen magance duk wata sata da ta shafi yanar gizo.