Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Kori Karar Matasa Kan Sauyin Yanayi


Masana Kimiya da Fasaha a Amurka sun ce sinadarin iskar gas dake fita daga shuke shuken da ake yi a fadin kasar na cikin abubuwan dake haddasa sauyin yanayi.

Za a sake daukaka karar da wasu matasa suka yi, sakamakon korar karar su da aka yi na da'awar ka'idojin yanayi da gwamnati ta yanke cikin kankanin lokaci. Hakan kuma zai janyo tsaiko da ci baya na bibiyan hukuncin doka a madadin matasa da yancin su a cewar masanan.

Wani alkali ne ya kori karar da matasan suka shigar a kotun ranar Talata, inda suke jayayyar cewa dole ne Jihar Washington, ta kara yin wani abu domin rage sinadarin carbon da ke fita mai kashe itattuwa da fure, tare da janyo illa ga al'umma. Alkalin ya ce wannan lamari na 'yan siyasa ne ba na kotuna ba.

Hukuncin da alkalin ya yanke, shine karo na farko da kotu ta kori karar da matasa suka yi, suna bukatar hukumomi su kara himma wajen dakile matsalolin sauyin yanayi, inda suke cewa ana keta hakokin yancin da dokar kasa ta basu a cewar masanan. Wata Lauya dake aiki da kungiyar, Andrea Rodgers ta fadawa kungiyar Thomson Reuters Foundation cewa zasu daukaka kara.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG