Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauyin Shekar Siyasa Ga Matasa Da Ra'ayoyin Iyayen Gida - Kwamared Sani Bala


Kwamared Sani Bala Tela
Kwamared Sani Bala Tela

A yau dandalinVOA zai dora ne da hirar mu da matashi kuma dan gwagwarmaya a harkar siyasar matasa wato Kwamared Sani Bala wanda aka fi sani da Sani Tela, dangane da matsalar da matasa ke fuskanta a sakamakon sauyin ra’ayi a siyasa wanda ke da nasaba da matsalar sauyin jamiyyar iyayen gida.

Rashin shugabanci shine ummul uba’isun gurbancewar siyasa a mulkin siyasar Nijeriya, ya ce lokaci yayi da matasa zasu farga su san cewar a siyasa an daina mahaukaciyar soyayyar akida.

Tela ya ce ko da matasan da ake ikikarin an basu dama a mulkin siyasa ba matasan da suka cancanta bane, yawanci ‘ya’yan iyayen siyasa ne ko kannen matan shugabanni da makamantan su, haka ake boyewa da sunan an ba matasa dama.

Ya ce ko da an dauki matashi an bashi mukami bai wuce mai bada shawara ko kuma mai kula da wasu harkoki da wuya kaga an ba matashi wani mukami da zai fada a ji.

Daga karshe ya ce yanzu aski ya zo gaban goshi, bai kamata matasa su yarda a danne masu hakki ba, ya kamata matasa su fito da babbar murya domin tabbatar da wajewa da shugabani cewar duk wanda ya sami madafar iko zai ba matasa kaso hamsin cikin dari na kujerun majalisar sa kuma matasan da suka cancanta ba ‘yan uwa ko ‘ya’yan abokai ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:21 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG