Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karya Furetake Bata 'Ya'ya: Wani Matashi Yayi Ma Kamfanin Apple Kutse


Wani matashi dan kasar Australia mai shekaru 16, ya amsa laifin sa na satar bayanai a runbun ajiyar bayanan kamfanin Apple, rahoton ya bayyana cewar matashin ya nadi bayanan jama’a wanda ya kwashe tsawon shekara daya yana shiga runbun bayanan kamfanin dan daukar bayanan sirri na jama’a.

Ya nadi bayanai da suka kai yawan gigabite casa'in 90, matashin da yake zaune a karamar hukumar Melbourne, kamfanin dillancin labarai na The Age newspaper. Ya bayyana cewar matashin ya saci bayanan ta hanyar amfani da manhajar ‘hacky hack hack.’

Kamfanin dai na Apple ya tabbatar da cewar babu wasu bayanan jama’a da aka dauka don yin wani abu dasu, kamfanin ya kara da cewar yana kokarin ganin cewar babu wani da zai iya shiga shafin kamfanin don satar bayanai, domin kuwa kamfanin na daukar kwararan matakai da suka dace wajen ganin ya tsare bayanan jama’a.

Don haka satar bayanan da matsahin yayi bai da wata tasiri domin kuwa bai iya daukar bayanan ta yadda zai iya amfani da suba ko sayar dasu ga wasu miyagu. Kana kamfanin zai kara bincikar yadda sakacin ya auku, da kuma alkawalin sanar da mahukunta.

Kamfanin ya nuna rashin jin dadin sa da kuma daukar duk wani laifi da hakan ya jawo, kana yana mai tabbatar ma abokan hurdar sa cewar wani abu makamancin haka ba zai sake aukuwaba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG