An Kai Muhimmin Mataki A Binciken Musabbabin Mutuwar MohBad – Lauya

MohBad

A cewar lauyan gwamnati O. Akinde, yanzu ana kan bincike kan sassan cikin jikin mawaki wanda shi ne mataki mafi muhimmanci.

Masu gudanar da binciken musabbabin mutuwar mawakin Afrobeat Ilerioluwa Aloba da aka fi sani da Mohbad, sun ce ana kan gudanar da binciken.

Lauyan Gwamnatin jihar Legas, O. Akinde, ya fadawa wata kotun Majistire cewa an kammala bincike kan sashin wajen jikin marigayin.

A cewar Akinde, yanzu ana kan bincike kan sassan cikin jikin mawaki wanda shi ne mataki mafi muhimmanci.

Binciken na gudana ne a Amurka a cewar lauyan.

A ranar 12 ga watan Satumba MohBad ya rasu cikin wani yanayi mai sarkakiya a Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

An binne shi a ranar 13 ga watan Satumba. Amma bayan korafe-korafe da ke nuna alamun akwai alamar tambaya kan mutuwar mawakin, hukumomin jihar ta Legas suka sa aka tono gawarsa.

A baya an kama mawaki Naira Marley da abokinsa Sam Larry wadanda ake zargin sun taka rawa wajen kuntatawa MohBad.

A ranar 6 ga watan Nuwamba aka ba da belinsu akan Naira Miliyan 20 kowannensu.

Naira Marley da Larry sun musanta zargin da ake musu.