Ana Fuskantar Matsalar Karancin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Nijar

Na'urar samar da wutar lantarki

Wasu ‘yan Nijar sun ce har yanzu mahukuntan kasarsu ba su dauki darasi ba, tun katse musu wutar da Najeriya ta yi tsawon watanni 8 bayan juyin mulki a karshen watan Yulin 2023.

An fuskantar matsalar daukewar wutar lantarki a baya-bayan nan a jihohin Jamhuriyar Nijar, sanadiyar lalacewar wadansu na'urori a jihar Kebbi da ke Najeriya, wadda ke bai wa kasar ta Nijar wutar lantarki, kamar yadda kamfanin watsa wutar lantarkin kasar Nigelec ya sanar.

Wasu ‘yan Nijar sun ce har yanzu mahukunta ba su dauki darasi ba, tun katse musu wutar da Najeriya ta yi tsawon watanni 8 bayan juyin mulki a karshen watan Yulin 2023.

Tun lokacin gwamnatocin da suka gabaci na sojan kasar a yanzu, sun ayyana kokarin su na jawo wutar lantarki mai aiki da man Diezel daga matatar man kasar SORAZ, da zai raya jihohin Zinder, Maradi da ma Tahoua, hasali ma, da girka wata tashar watsa wutar lantarki da hasken rana a garin Malbaza, sai dai har yanzu ana iya cewa da sauran rina a kaba.

Alhadji Jafaru Dubai ya ce ma’aikatar wuta ta Nijar gaba daya suna kokarin gaskiya, saboda suna samu su dan rabawa mutane wuta duk da matsalolin da akai ta samu.

Kuma yanzu idan aka duba Zinder da Maradi suna samun wutar da aka yi kokari aka hada cikin kasar.

Da yake amsa ko mene ne ke kawo tafiyar hawainiya a kasar game da samun wadatacciyar wutar lantarki? Asemi Ciroma na kungiyar Rotab, mai saka ido ne a harkokin makamashin wutar lantarki, ya ce gwamnati ba ta sa kudade a wajen tanadar da makamishin sai wasu kamfanin can ko kuma Najeriya ta tanadar da shi ta sayar musu, su kuma kamfanin na Nigelec ya saida wa ‘yan kasarsu.

Game da kokarin da gwamnatin kasar ke yi domin warware wa yan kasar matsalar wutar lantarki, gwamnan jihar Tahoua, Kanal Umaru Tawaye, tare da ministan makamashin kasar sun kai ziyara a wurin kamfanin kasar Birtaniya SAVANA ENERGY da wadansu ‘yan kasar Nijar ke kokarin girka turakan watsa wutar lantarki mai aiki da bugawar iska tsakanin Madaoua da Malbaza a cikin jihar Tahoua.

Gwamnan jihar ta Tahoua, ya ce sun sha wahala kan harkar lantarki kuma suna godiya.

A cewar Abbas Bawa mai sharhi a kan harkokin da suka shafi makamashi, samun ‘yancin kan Nijar a fannin wutar lantarki, zai taimaka, domin samarwa matasa ayyukan yi da yaki da talauci a cikin kasar.

Wutar lantarki ta kasance daya daga cikin ababen more rayuwa da kowane dan kasa kan yi fatan samu domin inganta rayuwarsu ta yau da kullum.

Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Fuskantar Matsalar Karancin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Nijar