Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta kaddamar da hare-haren ne kan arewacin kasar Isra'ila a yau Talata, inda ta yi gargadin cewa martanin da aka jima ana jira na nan tafe bayan da Isra’ilar ta kashe wani babban kwamandanta a makon da ya gabata.
Hezbollah ta ce ta kaddamar da wani harin jirage sama mara matuka ne a wasu wuraren soji guda biyu da ke kusa da Acre a arewacin Isra'ila, sannan ta kai hari kan wata motar sojin Isra'ila a wani wuri.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an gano wasu jirage mara matuka da suka tsallaka daga kasar Lebanon sannan aka kama guda daya.
Ta ce an jikkata wasu fararen hula a kudancin birnin Nahariya da ke gabar teku.
Hotunan gidan talabijin na Reuters sun nuna wani wurin da ke da tasiri a kusa da tashar ba sa kan babbar hanyar da ke wajen birnin.
-Reuters