Ana Ci Gaba Da Samun Sakamako Na Bazata A Qatar: Japan Ta Ba Jamus Mamaki Da Ci 2-1

Dan wasan Japan Ritsu Doan a Qatar

Kwallayen da Ritsu Doan da Takuma Asano suka ci bayan da suka shigo wasa cikin minti 15 na karshe, sun bai wa Japan damar ba da mamaki inda ta yi wa Jamus mai rike da kofi har sau hudu ci 2-1 a gasar cin kofin duniya da suka buga ranar Laraba. 

Da farko ‘yan kasar Jamus ne suka buga wasa mai kyau a gasar kwallon da aka yi a filin wasa na Khalifa International Stadium inda Ilkay Guendogan ya zura kwallo a bugun fenariti a daidai minti na 33 bayan da golan Japan Shuichi Gonda ya yi wa David Raum keta.

Mamaye wasan karo na biyu bai yiwu ba ga Jamus, a zagaye na biyu Japan ta buga wasa mai kyau inda ta kai hare-hare da a karshe suka ba Doan da Asano damar zura kwalaye.

Wannan shi ne karo na uku a jere da aka lallasa Jamus a wasanni farko na babbar gasar cin kofin kwallo, bayan da ta sha kashi a hannun Mexico a gasar cin kofin duniya ta 2018, lokacin da ta sha kayi a matsayin mai rike da kambi da kuma lokacin da ta sha kayi a hannun Faransa a gasar cin kofin nahiyar ta 2020 ta Euro 2020.

Kasar Croatia wadda ta zo ta biyu a gasar cin kofin duniya da ya gabata, ta yi baram baram da Morocco inda aka tashi da ci 0-0 a filin wasa na Al Bayt ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba a wasan farko na rukunin F na gasar da ake yi a Qatar.