Mun kusa amincewa kan batutuwa biyar ko shida. Akwai sauran abubuwa da yawa a nan gaba. Kuma ba ma kan yarjejeniya a wadannan abubuwan biyar ko shida, amma a kalla sun fahimci bukatun mu, "Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Chuck Schumer ya fadawa manema labarai a jiya Talata.
Chuck Schumer Tare da kakakin majalisar Nancy Pelosi, sun shirya don ganawa da Sakataren baitul malin Amurka Steven Mnuchin da shugaban ma'aikatan fadar White House Mark Meadows.
Bangarorin biyu sun rarrabu akan batun girman shirin tallafin da suka gabatar, yayin da 'yan jam'iyyar Democrat ke kiran a fitar da dala tiriliyan 3.4 , su kuma 'yan Republican suka ce dala tiriliyan daya.
Daga cikin abubuwan da ake tattaunawa akwai tura wani zagaye na tallafin kudi, da taimaka wa masu haya don gujewa kada a kore su, da taimakawa ma'aikatar aikewa da sakwanni da kuma $600 duk sati na rashin aikin yi wanda ya kare a makon da ya gabata.
Shugabannin Republican suna son a yi karamin shirin ba da tallafi wanda zai magance wasu abubuwa yayin da suka bar tattaunawa daga baya. ‘Yan Jam’iyyar Democrat sun yi watsi da wannan, suna ba da hujjar cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dauki babban mataki don tunkarar kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.