Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Zabe A Wasu Yankunan Jos A Jihar Filato

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Zabe A Wasu Runfuna Na Jos, Jihar Filato

Rumfunan zabe da dama ne zasu ci gaba da gudanar da zabe a yau Lahadi a cikin birnin Jos, na JIhar Filato.

PLATEAU, NIGERIA - Duk da yake hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Jihar Filato ba ta fito da sanarwa ko amsa kira ko sako da muka aika wa Jami'inta Malam Shehu Baba ba, rumfunan zabe da dama a yankin "Narguta B" da ke karamar hukumar Jos ta Arewa ba su kammala zaben a jiya Asabar ba.

Wasu da muka zanta da su kan matsalolin da suka kawo tarnaki wa zaben sun bayyana rashin zuwan jami'an zabe da kayan aiki a kan lokaci, da matsalar na'urar tantance masu kada kuri'a, BVAS, wanda kan yi zafi ya kuma daina aiki.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ayyana ci gaba da gudanar da zaben a wassu Jihohi goma sha biyar da birnin tarayya Abuja, sai dai bai sanya Jahar Filato a cikin jihohin da za'a ci gaba da zaben na yau Lahadi ba.