Ana Bukatar Gidauniyar Tallafawa Wadanda Boko Haram ta Rutsa da Su

Ginin Majalisar dokokin Amurka

Wasu 'yan majalisar wakilan Amurka sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa gidauniyar tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su.
Yayin da suke jawabi a dandalin da wasu 'yan Najeriya ke zaman durshen neman a sako 'yan matan Chibok, 'yan majalisar wakilan Amurka sun bukaci a kafa gidauniyar da zata tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su.

A jawabinsu sun ce sun san 'yan matan Chibok na hannun 'yan Boko Haram, kungiyar dake kai hari akan wuraren ibada ba tare da banbance kowane addini ba.

'Yar majalisa Sarah Jackson Lee daga jihar Texas tare da abokan aikinta uku suka yi jawabi a dandalin Unity Fountain dake Abuja inda aka fara kemfen din a dawo da 'yan matan Chibok ya fara. 'Yan majalisar sun bukaci gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wata gidauniya da zata tallafawa da biyan diya ga duk wanda rikicin Boko Haram ya rutsa da shi, ko danginsa.

Sun ce sun gani da kansu daga labaran da sojojinsu suke basu akan yadda ake cin zalin al'umma sabili da haka suna ganin kaddamar da gidauniyar domin tallafawa iyalan wadanda aka kashe ya zama wani abu mai mahimmanci.

A cewarsu, Amurka ta ware miliyoyin daloli domin kwato 'yan matan Chibok da kuma tallafawa gwamnatin Najeriya domin kwantar da fitinar. Sun ce saboda tsananin talauci a Najeriya yasa fatar yara da matasa ta dusashe lamarin da ya jefasu aukawa cikin ta'adanci har ma suna ganin rayukansu basu da wasu mahimmanci.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Bukatar Gidauniyar Tallafawa Wadanda Boko Haram ta Rutsa da Su - 1'22'