Ana Bincikar Mutuwar Masu Zanga-zanga Bakwai a Zimbabwe

An fara gudanar da binciken musabbabin mutuwar a kalla mutane bakwai a cikin wata zanga zangar bayan zaben kasar Zimbabwe.

Adrian Munjere yayi hira da Muryar Amurka bayan da ya bada bahasi gaban kwamitin binciken.

Ina bakin cikin abin dake faruwa. Ina fata za a biya ni diyya, saboda yanzu haka bana iya amfani da wannan hannu wajen yin aiki ko kuma daukar wani abu mai nauyi. Ba wai diyar da nake son zai magance wannan lahani da aka min bane, babu. Kawai dai saboda taimakon rayuwata.

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya kafa wata hukuma mai zaman kanta, karkashin jagorancin tsohon shugaban Afrika ta Kudu Kgalema Motlanthe.

An ba hukumar wa'adin watanni uku ta kammala aikinta ta kuma sa a kawo karshen batun harbe harben, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane akalla bakwai wasu da dama kuma suka ji rauni.