Aikin zai lakume sefa biliyon 180, kuma, tun ranar 23 ga watan Aprilun 2014 ne shugaban kasar Nijer Alhaji Mahamadu Isuhu ya jagoranci bukin aza tubali na farko na gina wannan kamfanin.
Kafa wannan kamfanin yana da muhimmanci a yankin kasancewa zai samar da ayyukan yi da kuma kara habaka tattalin arziki cikin gaggawa. An bayyana cewa, mutane dubu biyu zasu sami ayyukan din-din-din a kamfanin simintin, yayinda wadansu mutane dubu uku zasu samun ayukan lokaci zuwa lokaci
Haka kuma ta dailin kafa wannan kamfanin simintin, kamfanin Dan Gotte zai gina makarantu, hanyoyi, rijiyoyi da samar da sauran ababan more rayuwa.
Da farko, kamfanin simintin zai rika samar da ton miliyan 1 na siminti a kowace shekara, daga bisani a kai ton miliyon 2 da rabi. Za a kuma sayar da kowanne ton a kan jikka 100 na sefa…
Binciken ya nuna cewa duk da yake an dade da fara harkokin siminti a Jamhuriyar NIjar, duk da haka kimanin kashi ishirin cikin dari ne kadai ake iya biya ta bukatar taki a kasar.
Saurari cikakken rahoton Haruna Mamman Bako:
Facebook Forum