Frank wanda tuni Jam'iyyar ta APC ta dakatar da shi don irin kalaman da ya ke yi na adawar cikin gida, ya bayyana a wata budaddiyar wasika ga Shugaba Buhari cewa, tubalin canji da gwamnatin da ginu akai tuni ya kama hanyar rugujewa a saboda rashin mutunta hakkokin jama'a - wanda yasa har wasu na nadamar zaben gwamnatin.
Frank ya ce rashin bin ka'idojin sanin ya kamata ko kare hakkin kowa a dimokradiyya, ya mayar da gwamnatin tamkar ta kama karya ko mulkin soja don haka ya bukaci Buhari ya dauki matakin bincikar gaskiyar lamarin da kansa.
Frank shine tsohon mataimakin Lai Mohammed a sashen watsa labarai na Jam'iyyar mai mulki gabanin nada Mohammed a matsayin ministan labarai inda Frank bai sami damar maye gurbinsa ba kai tsaye. Daga nan kuma ya sauya zuwa dan adawar cikin gida na jam'iyyar har ma da ambatar kansa a matsayin sakataren watsa labarai daga bisani jam'iyyar ta nada Bolaji Abdullahi a matsayin wanda ya maye gurbin Mohammed - ta bar Frank da sallallami.
Wasu na sukar yadda ake tafiyar da yaki da cin hanci da rashawa inda suke ganin cewa ana 'yar mowa da 'yar bora ne a harkar - idan har shugaban kasa ya yarda da kai, duk irin laifin da ka yi, kai ba mai laifi ba ne. Idan kuma hankalinsa bai kwanta da kai ba, komin kirkinka, kai ba mai kirki ba ne, a cewar Shugaban kungiyar raya matasan arewa, Imran Wada Nas.
"An yi wani tsohon sakataren gwamnati, matasa mun yi ta kukan abubuwan da yayi, amma ba a cireshi ba har sai da aka ga rai zai bace. Sannan bayan an cireshi, ba a tsareshi ko gurfanar da shi ba. Wani kuma da yayi gwamna da minista, an ta bin shi ana laluben gano laifin da yayi kawai don ana ganin ya na da niyyar son tsayawa takara." inji Wada Nas
Ya kara da cewa idan har ana son a yi maganin cin hanci da rashawa, to dole sai an koma wanda duk yayi a yi mashi, ba sani ba sabo.
Shi ko babban sakataren Jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ya yi watsi da ire-iren wadannan sukar da nuna cewa gwamnatin na kan turba.
"Idan akwai abinda muka sa a gaba shine, kyautata rayuwar 'yan Najeriya, da maido da mutuncin Najeriya ta dawo kamar yadda ta ke. Wannan shine burin Shugaba Buhari."
Saurari cikakken rohoton Nasiru El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5