Mai Martaba Dr.Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shugaban majalisar sarakunan jihar ya nuna takaicinsa game da abubuwan dake faruwa a Najeriya, na tashe tashen hankula, ya ce dole kowa ya zama jami’in tsaro,musamman idan aka yi lakari da yadda yan ta’adda da kuma bata gari kan sauya salo ayanzu.
Lamidon yace, muddin yan Najeriya zasu zura ido ne kawai su jira jami’an tsaro su kawo musu dauki,to za’a dade ba’a je ko ina ba. Ya ce “ina kira ga jama’a su tashi tsaye su taya gwamnati wajen sa ido da kuma lura da wurare da jama’a ke taruwa. A tsare masallatai da mijami’u da makarantu da kasuwanni da dai sauransu. Haka ma mutanen da ba’a yadda dasu ba kada a yi tantama a sanar da jami’an tsaro.”
Yace alama ta nuna damina zata yi kyau saboda haka ya yi kira ga jama’a su koma ga aikin gona. Akan wannan dalili, ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta gaggauta wadata manoma da ingantattun iri da takin zamani da maganin kashe kwari da kuma taraktoci.
A jawabinsa gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, tilawa ya yi na irin kokarin da ya ce gwamnati ke yi a yanzu wajen fidda dan duma daga kabewa. Babu abun da ya dameshi kamar batun samun hanya saboda ita ce zata kawo bunkasar tattalin arziki. Yace nan da shekara daya zasu kammala aikin hanya kana su fuskanci wani abun daban kamar maida hankali akan noman shinkafa. Ya ce jihar ce ta fi kowace jiha kasar noman shin kafa.
A bana dai in banda yankin Madagali da kan samu hare-haren sari-ka-noke ba, an kammala shagulan sallan na kwanaki uku cikin tsanaki, da kuma tsauraran matakan tsaro.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum